Shugaban Ukraine Zelenskyy Ya Tafka Wani Hatsarin Mota,

Alfijr ta rawaito Motar shugaban kasar Ukraine Volodymyr Zelenskyy ta yi karo da wata motar bayan wata ziyarar da ya kai a fagen fama, amma bai samu wani mummunan rauni ba, in ji kakakinsa.

Alfijr Labarai

Zelenskyy yana komawa Kyiv ne daga yankin Kharkiv, inda ya ziyarci dakarun da ke birnin Izium da aka kwato.

Kakakin shugaban Sergii Nikiforav, ya bayyana haka a shafinsa na Facebook cewar, Wata motar fasinja ta yi karo da ayarin motocin shugaban a babban birnin Ukraine.

Direban motar ya sami taimakon farko daga tawagar likitocin Zelenskyy, kuma motar daukar marasa lafiya ta dauke shi, in ji shi.

Likitoci sun binciki shugaban, wanda bai samu wani mummunan rauni ba, Nikiforov ya rubuta.

Alfijr Labarai

Bai fayyace irin raunin da Zelenskyy ya samu ba.

Kakakin ya kara da cewa, ana gudanar da bincike kan lamarin.

Zelenskyy ya makara wajen buga adireshin bidiyo na dare da ya bayar a lokacin yakin, watakila saboda hadarin mota.

Slide Up
x

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *