ShugabaTinubu ya amince a sauyawa gidajen gyaran halin 29 matsuguni a Najeriya

IMG 20250212 WA0210

Shugaban kasa Bola Tinubu ya amince da sauyawa gidajen gyaran hali guda 29 matsuguni a sassan Najeriya.

Ministan kula da harkokin cikin gida Olubunmi Tunji-Ojo ya bayyana hakan a yayin da yake mika sabbin motoci 39 da wasu kayan aiki ga jami’an hukumar gidajen gyaran hali a Abuja.

Tunji-Ojo ya kara da cewa, da yawa daga cikin gidajen gyaran da ake da su, kamar na Suleja da Ikoyi, da sauransu,an kafa su ne a shekarun 1950 kuma sun tsufa.

Yace irin wadannan gidajen gyaran hali na Najeriya sun shiga cikin gari, wanda yace Shugaban kasa Bola Tinubu ya amince a mayar dasu wajen gari.

Daga nan ya shaida cewa nan gaba za’a lissafo gidajen gyaran halin da za’a sauyawa matsuguni daga cikin gari zuwa wajen gari a sassan kasar nan.

Ministan ya jaddada bukatar yiwa gidajen gyaran halin guda 29 garambawul bayan na fitar dasu zuwa wajen gari domin inganta yanayin walwalar fursunoni.

Ya kara dacewa hakan kuma zai rage cunkoson daurarru da kuma tabbatar da tsaro.

Da ya juya akan karin girma da aka yiwa jami’an hukumar,ministan yace a cikin watanni 24, an yi wa sama da mutane 50,000 karin girma a hukumar.

A nasa bangaren, mukaddashin Shugaban hukumar kula da gidajen gyaran hali na Najeriya Mr. Sylvester Nwakuche, ya ce za a raba sabbin motocin ga ofisoshin hukumar a jihohin da akafi bukatarsu.

TST Hausa

For more information about  Alfijir labarai/Alfijir news follow here  👇

https://twitter.com/Musabestseller?s=09

https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165

https://www.threads.net/@alfijirlabarai

https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12

https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag

Alfijir labarai Alfijir News Whatsapp Group 👇👇

https://chat.whatsapp.com/IqPyC2oGzdQ9NudcMXFqHZ

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *