Silar Mutuwar Aurena Da Sani Musab Danja! Inji– Mansurah Isah

Alfijr ta rawaito Mansurah Isah tace  mutuwar aurenta da jarumi Sani Musa Danja ba komai bane fa ce  ƙaddara ce daga Allah, a karon farko tun bayan mutuwar auren nata shekera daya da rabi

Alfijr Labarai

Mansura ta bayyana cewa tun bayan rabuwar su da Sani ta ke ganin maganganu daban daban kan al’amarin a shafukan sada zumunta, inda har wasu su na zagi, wasu kuma na nuna ɓacin rai a game da rabuwar tasu.

Jarumar wadda ke da yara huɗu da Sani Danja, mace ɗaya, maza uku, ta ce ko da farko ma abin da ya sa ta sanar da duniya labarin rabuwar su, ta yi hakan ne domin kada a matsayin ta na fitacciya a gan ta a wani waje ko ta tsaya da wani, a riƙa yi mata kallon da bai dace ba

Ta ce: “Na san mutane su na sha’awar zaman auren mu, har ma ana kafa misali da mu a cikin ‘yan fim da mu ka shafe tsawon lokaci mu na zaman aure, don haka rabuwar ba ta yi wa kowa daɗi ba. 

“To amma mutane su sani, duk rashin jin daɗin su, mu mun fi su rashin jin daɗin hakan saboda mu ne mu ke zaune da juna kuma mu ka rabu.

Alfijr Labarai

Mun yi aure ba ne don mu rabu ba, mun kuma  shafe shekaru goma sha huɗu mu na tare, don haka Allah ne ya kawo ƙarshen zaman mu babu yadda muka iya, ko muna so ko bama so.

Muna mutuwar godiya ga yadda masoya ke nuna damuwa, kuma su ke yi mana fatan alheri, mu ma mu na yi masu.

“Kuma ina ba su haƙuri da ƙaunar da su ke nuna mana, masu zagi kuma su je su yi ta yi, ba za mu hana su ba.”

Auren Sani da Mansurah, ya mutu ne a ranar 27 ga Mayu, 2021, bayan tsohuwar jarumar ta wallafa sanarwar rabuwar su a shafinta na Instagram, saƙon da ta goge bayan minti kaɗan.

Alfijr Labarai


Kamar yadda mujallar Fim ta wallafa