Rundunar Sojan Ruwa Ta Kama Kwale-kwale Da Muggan Kwayoyin Miliyan N200

FB IMG 1696546333977

Rundunar sojin ruwan Nijeriya ta kama wani Kwale-kwale dauke da wasu kulli da ake zargin muggan kwayoyi ne a Ibeshe, Iworo da Badagry a jihar Legas.

Alfijir Labarai ta rawaito wata sanarwa da jami’in yada labarai na rundunar, Sub Lieutenant Happiness Collins ya fitar, ya ce, a kiyastacce, kwayoyin sun kai Naira miliyan 200, nauyinsu ya kai kilo 2,640.

Duk da cewa, wadanda suka yi kokarin shigowa da kayan, sun tsere bayan hango jami’an sojin, amma an kwace kayayyakin tare da mika su ga hukumar hana sha da fataucin miyagun kwayoyi ta kasa (NDLEA) domin daukar matakin da ya dace.” inji sanarwar.

Collins ya kuma bayyana cewa, Kwamandan rundunar sojin ruwan da ke sintiri a yankin (NNS BEECROFT), Commodore Kolawole Oguntuga, ya bukaci jama’a da su ci gaba da bayar da rahoton sirri ga jami’an tsaron domin dakile ayyukan ‘yan ta’adda.

Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a

https://twitter.com/Musabestseller?s=09

https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165

https://www.threads.net/@alfijirlabarai

https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12

https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag

Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijir Labarai  👇

https://chat.whatsapp.com/FNim39ly65N2CzcTt8FgWb

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *