Sojojin Nijar Sun Umarci Ƴan Sanda Su Fitar Da Jakadan Faransa Daga Ƙasar

Sojojin sun ce jakadan Nijar ya yi amsa gayyatar da suka yi masa.

Alfijir Labarai ta rawaito sojojin Nijar sun kwace kariyar diflomasiyya da jakadan Faransa yake da ita sannan suka umarci ‘yan sanda su fitar da shi daga kasar.

A makon jiya ne sojojin, wadanda suka kifar da gwamnatin Mohamed Bazoum, suka bai wa jakadan Faransa Sylvain Itte wa’adin awa 48 ya fitar daga kasar.

Wa’adin ya kare ranar 28 ga watan Agusta amma Itte ya ci gaba da zama a Yamai.

Shugaban Faransa Emmanuel Macron ya ce kasarsa ba ta amince da sojojin ba saboda ba ta halastacciyar hanya suka karbi mulki ba, yana mai cewa jakadansu zai ci gaba da zama a Nijar.

Hasalima ya jaddada goyon bayansa ga hambararren Shugaba Mohamed Bazoum, wanda ya yaba wa saboda kin yarda ya yi murabus.

Wata wasika da Ma’aikatar Harkokin Wajen Nijar ta fitar a wannan makon wadda kamfanin dillancin labarai na Associated Press ya gani ranar Alhamis ta ce daga yanzu Itte “ba zai samu kariyar da ake ba shi ba a matsayin ma’aikacin diflomasiyya.”

Wasikar ta ce an soke shaidar katin diflomasiyya da kuma biza na iyalansa.

TRT Afrika da abokan hulda

Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a

Facebook.   Alfijir Labarai
YouTube.     Best Seller Channel
Twitter.        @Musabestseller
Instagram.  @musa_bestseller

Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijir Labarai  👇

https://chat.whatsapp.com/Jmw5CBsPV6H3DbSgnlFUHM

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *