Sufeton Ƴan Sanda Nigeria Ya Gargaɗi Jami’ansa Kan Bin Dokar Tuki

Ya ce ya zama wajibi su rika bin doka kamar kowane dan kasa ke bi.

Alfijir Labarai ta rawaito Sufeto-Janar na ’Yan Sandan Najeriya, Olukayode Egbetokun, ya ba da umarnin cewa daga yanzu, ya zama wajibi ’yan sanda su rika tsayawa a danja har sai an ba su hannu kamar kowa.

Ya bayar da umarnin ne ranar Litinin, yayin wani taro da sashen ’yan sandan kwantar da tarzoma da ke hedkwatar ’yan sanda ta kasa a Abuja.

A cewarsa, ya zama wajibi rundunar ta bayar da kyakkyawan misali muddin tana so ta samu girma a idanun mutane.

Ya ce, “Kafin na kare wannan jawabin, ina so in tunatar da ku cewa dukkan wadanda aka dora wa alhakin tabbatar da zaman lafiya da kiyaye doka ya kamata su ma a ga suna bin ta sau da kafa.

“Idan ’yan sanda ba sa bin doka, su ma ba su da bakin da za su tilasta wa wasu su bi ta, ko ma su nemi hukunta su idan sun karya ta.

“A sakamakon haka, a kokarina na gina runduna mai bin doka, na bayar da umarnin cewa daga yanzu, duk wata motar ’yan sanda da ba aikin gaggawa take yi ba, ya zama wajibi ta bi dokokin kula da ababen hawa, kuma zan yi shugabanci na misali a wannan bangaren,” in ji shi.

Tun a lokacin da ya karbi ragamar rundunar a makon jiya dai, Egbetokun, ya yi alakawarin kawo sauye-sauyen da za su inganta hanyoyin da ake tafiyar aikin dan sanda a Najeriya.

Aminiya

Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a

Facebook.   Alfijir Labarai
YouTube.     Best Seller Channel
Twitter.        @Musabestseller
Instagram.  @musa_bestseller

Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijir Labarai  👇

https://chat.whatsapp.com/GdLiqZyHuSz5NhjdGoGRGZ

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *