Takaitattun Labaran Duniya Na Safiyar Asabar 09/03/2024CE – 28/08/1445AH

best seller i2

Daga Baba Usman Gama

Wasu ƴan bindiga sun kai hari kan ɗaruruwan Musulmai a yayin da suke sallar Juma’a a wani yanki na Birnin Gwari da ke jihar Kaduna.

Gwamnatin Tarayya ta tura sojoji domin ceto dalibai sama da 250 da aka sace a Kuriga.

Atiku ya nuna damuwa kan sace malamai, ɗalibai da ƴan gudun hijira a Borno da Kaduna.

Hukumar tsaro ta farin kaya (DSS) ta gargadi ƴan Najeriya da su guji cunkoson jama’a domin rage haɗurran da ka iya aukuwa.

Gwamnan Jihar Zamfara Dauda Lawal Dare, ya lashi takobin bin kadun kisan Malam Abubakar Hassan Mada da ake zargi rundunar tsaro ta gwamnatin jihar ta hallaka.

Allah ya kawo mu, Sarkin Musulmi ya bada umarnin a fara duba jinjirin watan Ramadan, 1445H ranar Lahadi.

Wasu miyagun ƴan bindiga sun halaka mutane 17 yayin da suka kai hari kauyen Mbaikyor Mbalom da ke ƙaramar hukumar Gwer a jihar Benuwai.

Kungiyar Amnesty tace yanayin da ake ciki a Najeriya Shugaba Tinubu ba shi da cikakken tsarin kawo ƙarshen ayyukan ƴan bindiga.

Unicef ta yi alla-wadai da sace ɗaliban Kuriga a jihar Kaduna.

ECOWAS za ta nemi masu su shiga tsakani kan lamarin Mali da Nijar da kuma Burkina.

An ji ƙarar fashe-fashe a kusa da cibiyar lantarki ta Zaporizhzhia dake Ukraine.

A wani yunkuri na hana yaduwar wata cuta an haramta sayar da nama a birnin Kampala na Uganda.

An gabatar da tsohon shugaban kasar Honduras kotu bisa laifin safarar miyagun kwayoyi.

Hatsarin jirgin sama ya kashe mutum bakwai a Burkina Faso.

La Liga: Barcelona ta sami nasara akan Mallorca da ci 1:0 a wasan jiya.

Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a

https://twitter.com/Musabestseller?s=09

https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165

https://www.threads.net/@alfijirlabarai

https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12

https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag

Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijir Labarai 👇

https://chat.whatsapp.com/CJ2q8cmhhOxFY6OEgwV5vk

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *