Takaitattun Labaran Duniya Na Safiyar Litinin 18/11/1445AH – 27/05/2024CE

Screenshot 20240317 131846 com.whatsapp.w4b edit 21836918129479

Daga Baba Usman Gama

Mataimakin Gwamnan Kano ta ba wa Mashawarcin Shugaban Kasa kan sha’anin Tsaro, Nuhu Ribadu, hakuri kan zargin hannunsa a yunkurin dawo da Aminu Ado Bayero kan kujerar Sarkin Kano.

‘Yan sanda a Kano, sun ce sun sami bayannan sirri  masu karfi  da suka yi zargin cewa  bata-gari na kokarin kai wa Majalisar dokokin Jihar hari.

Yara mata 2 sun rasu yayin da wasu mutum 5 suka samu raunuka a jiyaLahadi sanadiyyar rushewar wani masallaci a unguwar Papa Ajao da ke Legas.

An kashe 2 daga cikin Ɗaliban jami’ar jihar Kogi da aka sace a kwanakin baya.

Ribadu ya yi barazanar gurfanar da mataimakin gwamnan Kano a Kotu bisa zargin ɓata masa suna.

Wasu mutum shida ‘yan gida ɗaya sun rasu sakamakon hatsarin mota da ya rutsa da su a Jihar Gombe.

Cikin awa 24 alhazai 2 daga jihar Kebbi sun rasu a dalilin fama da ƴar gajeruwar rashin lafiya.

Gwamnatin Tarayya, ta kaddamar da aikin gina rukunin gidaje masu 1 da 2 da 3 ƙarƙashin shirin ‘renewed hope’ guda 250 a Jihar Gombe.

Kokarin cikarsa shekara daya akan mulki Gwamna Lawal ya ƙaddamar da manyan ayyuka a kananan hukumomin Zamfara.

Babbar jam’iyyar adawa a Afirka ta Kudu ta zargi jam’iyya mai mulki da gazawa a aiki.

Yan tawayen ADF sun sake kai hari kan fararen hula a gabashin DRCongo.

Jakadan Faransa a Sri Lanka da Maldives, Jean-François Pactet, ya mutu.

Manchester United ta tattauna da wakilan kocin Brentford Thomas Frank da kuma tsohon kociyan Chelsea Mauricio Pochettino, yayin da ake tunanin za ta iya korar Erik ten Hag.

Ɗan wasan Morocco Sofyan Amrabat, ya ce zai tattauna da Manchester United game da makomarsa, inda kulob ɗin na Old Trafford ke da zaɓin mayar da zaman aronsa daga Fiorentina zuwa na dindindin.

Southampton ta samu tikitin shiga Premier League ta 2024/25.

Laliga: Barcelona ta sami nasara akan Sevilla da ci 2:1 a wasan jiya.

Seria A: Atalanta ta sami nasara akan Torino da ci 3 0 a wasan jiya.

Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a

https://twitter.com/Musabestseller?s=09

https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165

https://www.threads.net/@alfijirlabarai

https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12

https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag

Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijr Labarai 👇👇

https://chat.whatsapp.com/F9mRRuOf58G3MlLKsNCJbL

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *