Takaitattun Labaran Duniya NaYammacin Talata 09/04/2024CE – 30/09/1445AH

IMG 20240103 WA0021

Daga Baba Usman Gama

Gwamnatin tarayya ta ƙara ranar Alhamis cikin ranakun hutun Sallah a Najeriya

EFCC, ta ce ta gano Naira biliyan 30 a wajen ministar ma’aikatar jin kai da aka dakatar, Betta Edu.

Sojoji sun tarwatsa sansanin ƙasurgumin ɗan fashin daji a Zamfara.

Gwamnan Katsina Radda ya biya wa fursunoni 222 tara albarkacin bikin sallah.

Ƴan sanda a Ribas sun kashe wasu da ake zargi ƴan ƙungiyar asiri ne.

Kotu a Kano ta sanya ranar 17 ga watan Afirilu domin gurfanar da tsohon gwamnan na jihar Ganduje Dan mutum 6.

Ali Nuhu ya gana da Jakadan ƙasar Spain Juan Ignacio, inda suka tattauna yadda Nijeriya da Spain za su haɗa hannu tare wajen inganta harkar fina-finai.

Allah ya yi wa fitacciyar ‘yar Kannywood, Saratu Daso rasuwa.

Gobara ta tashi a kasuwar Idomota, ɗaya daga cikin manya kuma daɗaddun kasuwannin Jihar Legas.

Gwamnatin jihar Neja ta haramta hawan dawaki a sassan jihar yayin bikin Sallah.

Sheikh Musa Ayyuba Lukuwa ya yi sallar idin ƙaramar sallah a jihar Sakkwato yau Talata.

Wani mutum ya yi yunƙurin kashe kansa a Masallacin Ka’aba.

David Cameron ya isa Amurka don tattauna batun ƙarin tallafi ga Ukraine.

Shugaban mulkin sojin Nijar janar Tchiani ya halarci Sallar idi.

Amurka ta sake yin kira ga Isra’ila da kada ta kai farmaki birnin Rafah.

Kotu ta amince Jacob Zuma ya tsaya takarar shugaban ƙasar Afirka ta Kudu.

Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a

https://twitter.com/Musabestseller?s=09
https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165
https://www.threads.net/@alfijirlabarai
https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12
https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag

Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijir Labarai 👇

https://chat.whatsapp.com/CJ2q8cmhhOxFY6OEgwV5vk

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *