Tallafi: Gwamna Ya Zaftare Farashin Man Fetur Zuwa Naira 500 Ga Kowacce lita.

IMG 20240311 WA0047

Daga Aminu Bala Madobi

“Muna so mu cigaba da samar da abinci ta hanyar amfani tsarin noma mai gajeren zango don magance matsalolinmu,

Alfijir labarai ta rawaito Gwamnan jihar Borno, Babagana Umara Zulum ya bayyana rage farashin litar man fetur ga manoman Damasak zuwa Naira 500 a kowacce lita a maimakon farashin kasuwan N730 domin bunkasa noman rani.

Zulum ya kuma kaddamar da wata tashar samar da ruwa mai amfani da hasken rana mai karfin doki 90 a Damasak a ziyarar aiki da ya kai garin a karshen mako.

Rahotanni sun ce tashar mai karfin doki 90HP, tana da hasken rana mai karfin kilowatt 115 da ke bada lantarki fannoni uku dasuka hadar da famfuna 30HP, tana fitar da lita 225 na ruwa a cikin dakika 105 mai dauke da hekta 125 na gonakin shinkafa.

Zulum ya bayyana cewa gwamnatin sa na maida hankali ne zuwa fannin inganta walwala dakuma cigaba da rabon abinci don karfafa ayyukan noma a jihar

“Muna so mu cigaba da samar da abinci ta hanyar amfani tsarin noma mai gajeren zango don magance matsalolinmu, sannan babu wani batu na tsugunar da wasu ‘yan gudun hijira. Don haka a shirye muke don cigaba da bada tallafin jinkai wanda kuma shine noma,” in ji Zulum.

Gwamnan ya bayyana cewa, za a samar da lita miliyan daya na man fetur ga manoma a karkashin shirin afadin kananan hukumomin jihar.

“Ina so in sanar daku cewa, a ayyukan noman rani na bana, gwamnatin jihar Borno za ta sayo lita miliyan daya na man fetur tare da raba shi a fadin jihar ga manoma.

“Bugu da kari mun sayo buhunan taki buhu 20,000, famfunan ruwa masu amfani da hasken rana 1,000 da kuma wasu injinan famfunan ruwa guda 5,000 da za a raba wa manoma a sassan kananan hukumomin uku na jihar Borno,” inji shi.

A ziyarar da yakai garin Damasak, Gwamna Zulum ya kuma raba takin zamani, injinan fanfo mai amfani da hasken rana tare da kayan aiki da kayan amfanin gona ga manoma a kananan hukumomi biyu.

Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a

https://twitter.com/Musabestseller?s=09

https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165

https://www.threads.net/@alfijirlabarai

https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12

https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag

Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijir Labarai 👇

https://chat.whatsapp.com/CJ2q8cmhhOxFY6OEgwV5vk

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *