TSAKA MAI WUYA! Israela Ta Garkame Dukkan Makarantun Kasarta

IMG 20240414 WA0018

Daga Aminu Bala Madobi

Biyo bayan yunkurin harin ramuwar gayya da kasar Iran ke shirin kaddamarwa ga kasar Israela, a yanzu haka Isra’ilan Ta Rufe Makarantu Saboda Matsalar Tsaro –

Alfijir labarai ta rawaito wasu hotuna da sojojin Isra’ila suka fitar ya nuna dakarun da ke kasa a zirin Gaza a ranar 7 ga watan Disamba, 2023, a ci gaba da fafatawa yaki tsakanin Isra’ila da kungiyar Hamas ta Falasdinu.

Isra’ila dai ta rufe makarantu a duk fadin kasar saboda tabarbarewar tsaro da ake cigaba da fuskanta sakamakon harin ramuwar gayya da kasar Iran ke shirin kaddamar wa, kamar yadda kakakin rundunar sojin kasar Daniel Hagari ya sanar a karshen mako.

Idan za a iya tunawa a ranar Asabar din da ta gabata, bayan da Iran ta yi barazanar mayar da martani kan wani mummunan harin da aka kai ofishin jakadancinta na Damascus.

“Za a rufe dukkanin makarantu kasar ne bisa la’akari da yanayin tsaro,” in ji shi a cikin wata sanarwa da aka watsa ta talabijin.

“Tun daga gobe da safe da kuma kwanaki masu zuwa, cibiyoyin ilimi, sansanonin shakatawa, da tafiye-tafiye an jingune su har sai abinda hali yayi” in ji shi.

Isra’ila za ta kuma takaita adadin mutanen da za su taru a waje zuwa 1,000, tare da adadi mafi karanci a yankunan kan iyaka, inda za a rufe bakin teku.

Ana gudanar da zanga-zanga mako-mako a Tel Aviv da Kudus don nuna adawa da gwamnati da kuma goyon bayan yarjejeniyar sakin mutane da aka dauke yayin turnukun fadar Hamas da sojojin israela.

Iran ta lashi takobin mayar da martani bayan harin da ake kyautata zaton Isra’ila ta kai a ranar 1 ga watan Afrilu wanda ya kai ofishin jakadancinta a Damascus, inda ya kashe jami’an kare juyin juya halin Musulunci bakwai ciki har da janar-janar guda biyu.

Shugaban Amurka Joe Biden ya fada a ranar Juma’a cewa yana tsammanin Iran za ta mayar da martani “da wuri (maimakon) daga baya”.

Tun da farko a ranar Asabar Dakarun kare juyin juya halin Musulunci na Iran sun kwace wani jirgin ruwan kwantena “mai alaka da gwamnatin Isra’ila a kusa da mashigin Hormuz, kamar yadda kafafen yada labarai na kasar suka ruwaito.

Ministan Harkokin Wajen Isra’ila, Isra’ila Katz, ya dage ziyarar da ya shirya zuwa kasashen Hungary da Ostiriya wanda aka shirya fara ranar Lahadi “saboda yanayin tsaro,” in ji kakakinsa.

Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a

Tohttps://twitter.com/Musabestseller?s=09

https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165

https://www.threads.net/@alfijirlabarai

https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12

https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag

Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijir Labarai 👇

https://chat.whatsapp.com/CJ2q8cmhhOxFY6OEgwV5vk

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *