Wani Ango Ya Kama Matarsa A Otel Tare Da Babban Abokinsa Mako Ɗaya Da Aurensu

Alfijr ta rawaito wani Ango ɗan Nijeriya da ya yi aure, ya kama matarsa tana tsaka da lalata da abokinsa Otal.

Alfijr Labarai

An ga wani faifan bidiyo da ya ɗauki hankulan mutane inda ya yaɗa matarsa da abokinsa a wani otel yayin da suke tsaka da holewar su. Rahotanni sun bayyana cewa ma’auratan sun yi aure kwanan nan, don haka abun ya matuƙar ɓata masa rai sosai inji shi angon.

Ango ya ce tun da farko ya gargaɗi abokin nasa mai suna Dennis da ya guji matarsa ​​bayan ya ga suna wata mu’amala wacce bai gane mata ba.

Amma sai bai ji ba, ya ci gaba ba har sai da na kama su da hannuna a wani ɗakin Otal inji shi.

Alfijr Labarai

A cikin faifan bidiyon, ana iya ganin shi yana caccakar abokin nasa wanda ya tarar da matarsa har ta ɓuya a banɗaki, in da Ango ya ke tambayar matar ta dalilin da ya sa ta ci masa amanarsa

RARIYA

Slide Up
x

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *