Wani Magidanci da ake zargi da kashe matar sa akan abincin buɗe-baki ya shiga hannun yan sanda a Bauchi

IMG 20250302 160333

Dqga Aisha Salisu Ishaq

Rundunar ƴan sandan jihar Bauchi ta ƙaddamar da bincike kan zargin wani magidanci da kashe matarsa saboda saɓanin da ya shiga tsakaninsu kan abincin buɗa-baki.

Alfijir labari ta rawaito cewa a wata sanarwa da kakakin rundunar, CSP Ahmed Mohammed Wakil ya fitar, ya ce lamarin ya faru ne a yankin Fadamar Mada da ke cikin garin Bauchi.

Ya ce, “saɓani ne ya kaure tsakanin wani mai suna Nuru Isah mai shekara 50 da matarsa ta biyu mai suna Wasila Abdullahi kan tsarin abinci da kayan buɗa-baki na gidan.”

Yan sanda sun ce binciken farko na nuna cewa mijin ya yi amfani da bulala wajen bugun matar, “inda ta yanke jiki ta faɗi, da aka kai ta asibitin koyarwa na jami’ar Tafawa Ɓalewa ne likitoci su ka tabbatar da rasuwarta.”

Sanarwar ta ƙara da cewa ƴan sanda sun kama mijin, sun ɗauko bulalar da aka yi amfani da ita, sannan kuma za a yi binciken ƙwaƙwaf a kan gawar.

Domin samun sauran shirye-shiryen Alfijir labarai/Alfijir news zaku iya bibiyarmu ta 👇

https://twitter.com/Musabestseller?s=09

https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165

https://www.threads.net/@alfijirlabarai

https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12

https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag

Alfijir labarai Alfijir News Whatsapp Group 👇👇

https://chat.whatsapp.com/IqPyC2oGzdQ9NudcMXFqHZ

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *