Wani Mara Lafiya Ya Sace Motar Ambulance A Kano

 

Wani Mara Lafiya Ya Sace Motar Ambulance  A Kano

Best Seller Channel 


Best Seller Channel 
Jami an ’Yan sanda sun kama barawon motar daukar marasa lafiyan ne a kauyen Takwasa na Karamar Hukumar Babura ta Jigawa a yayin da yake kokarin tserewa da ita.

Jaridar Aminiya ta rawaito, mai magana da Yawun rundunar ’yan sandan jihar Jigawa, ASP Lawan Shiisu, yace sun gano motar ce a kauyen Takwasa ta Karamar Hukumar Babura a Jihar Jigawa, a hannun wani mutum dan Karamar Hukumar Daura Jihar Katsina, dauke da karaya a kafarsa.”

Bayan samun rahoton, “sace motor r daukar marasa lafiya, Bus kirar ‘Hummer da magungunan da ke cikinta, mallakin Karamar Hukumar Ungogo ta Jihar Kano, a kauyen Kanya Hore da ke Karamar Hukumar Dawakin Tofa ta Jihar Kano, aka yi sa ar kama motar. 

Best Seller Channel 

Wannan nasara ta samu ne Karkashin ’Yan Sanda da ke Karamar Hukumar Babura ta Jihar Jigawa suka dukufa aiki, inda washegari suka gano ta da misalin karfe 8 na safiyar ranar Litinin 11 ga watan Disamban da muke ciki.

ASP Lawan ya kara da cewa ana ci gaba da gudanar da bincike kafin fa gurfanar da wanda ake zargin a gaban kotu don ya girbi abinda ya shuka.