Wani Mummunan Hadari Da Ya Afku Yayi Sanadiyyar Jikkatar Mutane 21

Alfijr ta rawaito hukumar kiyaye haddura ta kasa FRSC a Niger ta tabbatar da jikkatar mutane 21 a wani hadarin mota da ya rutsa da su a hanyar Bida zuwa Minna ranar Lahadi.

Alfijr Labarai

Kwamandan sashin Kumar Tsukwam, ya shaidawa kamfanin dillancin labarai na Najeriya NAN a ranar Litinin a Minna cewa, hatsarin ya afku ne da misalin karfe 9:25 na safe kusa da kauyen Sabon Gida a karamar hukumar Bida.

Ya bayyana cewa hatsarin ya hada da wata mota kirar Toyota Bus mai lamba NSR 540 ZG da wata mota kirar Range Rover mara rijista.

A cewarsa, mutane 21 ne suka shiga cikin hatsarin kuma dukkansu sun samu raunuka daban-daban.

Ya ce 14 daga cikin wadanda suka jikkata an kai su Cibiyar Kiwon Lafiya ta Tarayya ta Bida, yayin da sauran bakwai kuma aka kwashe su zuwa babban asibitin Umaru Sanda da ke Bida domin yi musu magani.

Alfijr Labarai

Kwamandan sashin ya ce hatsarin ya afku ne a lokacin da daya daga cikin tayoyin motar kirar Toyota ta fashe, sannan motar ta kutsa kai cikin babbar motar Range Rover da ke tafe.

Ya shawarci masu ababen hawa da su yi taka-tsan-tsan, su rika duba ababen hawansu yadda ya kamata kafin a dora su a kan hanya sannan kuma su bi tsauraran matakan da za su bi don guje wa hadurra.

Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a

Facebook. Best seller Channel
YouTube. Best Seller Channel
Twitter. @Musabestseller
Instagram. @musa_bestseller

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *