Wani Mummunan Hadari Ya Rutsa Da Mutane 10 Ƴan Gida Ɗaya Sun Mutu A Kano


Alfijr ta rawaito hukumar kiyaye abkuwar haɗurra ta Najeriya (FRSC), ta ce wasu mutane su goma ‘yan gida ɗaya kuma yan asalin jihar Kano sun mutu sakamakon hatsarin mota akan hanyar Kano zuwa Kachia da ke jihar Kaduna.

FRSC ta bayyana mutanen suna kan hanyar su ta dawowa ne garin Kachia, bayan sun halarci bikin ɗaurin aure a jihar Kano.

Kwamandan hukumar ta FRSC a jihar Kaduna, Zubairu Mato ya shaidawa manema labarai cewa, lamarin ya faru ne sanadiyar yunkurin da direbar motar golf din da mutanen yayi na shige wata mota wadda sanadiyar haka sitiyari ya kufce masa.

Ya kuma ce motar tana ɗauke da mutane goma ne, manya takwas da ƙananan yara biyu

Kwamandan hukumar na FRSC a jihar Kano ya kara da cewa hatsarin ya faru ne da misalin karfe biyar na yamma a ranar Lahadi a kauyen Makyelli.

Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a

Facebook. Alfijr Labarai
YouTube. Best Seller Channel
Twitter. @Musabestseller
Instagram. @musa_bestseller

Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijr Labarai 👇

https://chat.whatsapp.com/G1wNveF9mGU7jec5mWhFvZ

One Reply to “Wani Mummunan Hadari Ya Rutsa Da Mutane 10 Ƴan Gida Ɗaya Sun Mutu A Kano”

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *