Alfijr ta rawaito wasu ƴan bindiga da har yanzu ba a tantance su waye ba, sun kashe Lucky Idoko, shugaban matasan jam’iyyar APC a jihar Enugu.
Alfijr Labarai
Dayo Isreal, shugaban matasan jam’iyyar APC na kasa, ya tabbatar da kashe Idoko a wani sako da ya wallafa a shafinsa na Twitter ranar Lahadi.
Shugaban matasan APC ya ce “wasu ‘yan bindiga ne da ba a san ko su wanene ba ne suka kashe Idoko a ranar Asabar.
An kashe Idoko ne a Unadu a lokacin da yake gudanar da sana arsa ta haya da babur.
An bayyana cewa fasinjan da ya kai a kan babur din ya tsallake rijiya da baya.
Alfijr Labarai
“A jiya, wasu ‘yan bindiga da ba a san ko su wanene ba sun kashe daya daga cikin namu – Shugaban matasan karamar hukumar Igboezer ta Kudu, wani matashi mai kokari sosai.
Allah Ya baiwa Iyalansa Hakurin Hakuri Rasa Ya kuma warkar da Kasar mu. In Ji, Isreal kamar yadda ya wallafa a shafinsa na Twitter.
Marigayin wanda ya taba wakiltar al’ummar Unadu a matsayin kansila, har zuwa rasuwarsa shugaban matasan jam’iyyar APC ne a karamar hukumar Igbo-Eze ta kudu ta Enugu. Rahotanni sun bayyana cewa shi ne shugaban kungiyar ’yan banga a yankinsa.
Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a
Facebook. Best seller Channel
YouTube. Best Seller Channel
Twitter. @Musabestseller
Instagram. @musa_bestseller