Wasu Diloli Sun Yi Kashin Kunshi 193 Na Hodar Iblis A Hannun NDLEA


Alfijr ta rawaito Wasu ’yan kasuwa biyu sun yi kashin kunshi 193 na Hodar Iblis bayan shafe kwanaki uku a hannun jami’an NDLEA

Bayanai sun ce an cafke mutanen da ake zargin ne a Filin Jirgin Sama na Nnamdi Azikiwe da ke Abuja, a ranar 10 ga watan Mayu yayin shigowarsu Najeriya daga kasar Uganda su biyu.

Babafemi ne ya tabbatar da hakan cikin wata sanarwa da ya fitar a wannan Lahadin.

Ya ƙara da cewa an dade ana neman mutanen biyu ruwa a jallo wadanda ake zargi ba su da wata sana’a face safarar miyagun kwayoyi.

Bayan shafe kwanaki a hannun hukumar, daya daga cikinsu ya yi kashin kunshi 100 na Hodar Iblis wanda nauyinta ya kai kilo 2.137, yayin da abokin tafiyarsa ya yi kashin kunshi 93 na hodar mai nauyin kilo 1.986.

Kazalika, jami’an NDLEA sun kai samame wata mashayar miyagun kwayoyi a titin Bama da ke Sabon Gari da kuma Filin Wasa na Sani Abacha da ke birnin Kano, inda suka cafke mutane 160 dauke da miyagun kwayoyi daban daban-daban.

Haka kuma, hukumar ta cafke wasu mutum biyu a titin Kano zuwa Maiduguri da tarin miyagun kwayoyi da suka hada da kwayoyi 5,000 na tramadol.

Wannan na zuwa ne a yayin da jami’an hukumar suka cafke wasu mutum 25 a yankunan Tora Bora, Gwarinpa, Karmo, Kasuwar Garko, Bwari da sansanin ’yan gudun hijira na Kucigoro da ke Abuja.

Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a

Facebook.   Alfijr Labarai
YouTube.     Best Seller Channel
Twitter.        @Musabestseller
Instagram.  @musa_bestseller

Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijr Labarai 👇

https://chat.whatsapp.com/G1wNveF9mGU7jec5mWhFvZ

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *