Wat Sabuwar! Kungiyar Kwadago Ta Bayyana Ranar Fara Yajin Aiki A Nigeria

ALFIJIR 1

.Kungiyoyin kwadago a Najeriya NLC da TUC sun baiwa gwamnatin tarayya wa’adin Kwanaki 14 ta cika alkawurin da suka kulla ko su tsunduma yajin aiki a fadin Kasar.

Alfijir labarai ta rawaito Koken nasu ya samo asali ne daga rashin aiwatar da yarjejeniya 16 da aka kulla tsakanin kungiyoyin kwadago (NLC da TUC) da gwamnatin tarayya a ranar 2 ga Oktoba, 2023.

Shugabannin kungiyoyin NLC da TUC sun bayyana damuwarsu da cewa, duk da kokarin da kungiyoyin kwadago ke yi na inganta zaman lafiya a ma’aikatu, ga dukkan alamu gwamnati ba ta damu da wahalhalun da al’umma suke ciki ba .

NLC da TUC, a cikin wata sanarwa da suka fitar, sun koka da cewa “abin takaici ne yadda aka tilasta mana daukar irin wadancan matakan, amma rashin kula da walwalar ‘yan kasa da ma’aikatan Najeriya da kuma tsananin wahala ya sa ba mu da zabi sai mun yi haka.”

“Sakamakon wannan ci gaba tare da sanin muhimmancin tabbatar da tsaro da kare hakki da mutuncin ma’aikatan Najeriya da ‘yan kasa, kungiyar NLC da TUC sun ba da wa’adi ga gwamnatin tarayya da ta mutunta yarjejeniya cikin kwanaki 14 daga gobe, ranar 9 ga Fabrairu 2024.”

Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a

https://twitter.com/Musabestseller?s=09

https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165

https://www.threads.net/@alfijirlabarai

https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12

https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag

Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijr Labarai 👇👇

https://chat.whatsapp.com/H3iC9eVfJI012LJzvCQn5V

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *