Wata Miyar! Gwamnatin Nijar Ta Rage Farashin Man fetur A Kasar

FB IMG 1721336455687

Gwamnatin sojin Nijar ta sanar da rage farashin man fetur a fadin ƙasar.

Alfijir labarai ta ruwaito Gwamnatin ta rage farashin fetur ne ƙasa daga CFA 540 zuwa CFA 499, haka ma an rage farashin dan dizel zuwa CFA 618 daga CFA 668.

Gwamnatin ƙasar ta ce matakin zai soma aiki ne daga ranar 23 ga watan Yuli.

Gwamnatin sojin Nijar ta ce manufar rage farashin shi ne,  rage wa ƴan ƙasa raɗaɗi musamman samun sauki kan farashin sufuri da na kayayyakin masarufi na yau da kullum.

Sai dai masu nazari kan al’amuran yau da kullum na ganin ya kamata gwamnati ta ɗauki mataki na tabbatar da ganin ‘yan kasuwa a kasar sun sauko da farashin kayayaki

Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a

https://twitter.com/Musabestseller?s=09

https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165

https://www.threads.net/@alfijirlabarai

https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12

https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag

Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijr Labarai 👇👇

https://chat.whatsapp.com/ELQRQyq1zGn7zpAVP8DwNj

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *