Ministan tsaron Najeriya, Alhaji Mohammed Badaru Abubakar, ya yi murabus daga muƙaminsa a daren Litinin.
Bayanai daga mai ba wa shugaban ƙasa shawara kan yaɗa labarai da dabaru, Bayo Onanuga, sun tabbatar da cewa Badaru ya aike da takardar murabus ɗinsa ga Shugaba Bola Ahmed Tinubu a ranar 1 ga Disamba.
A cewar takardar, Badaru ya ce dalilin barinsa aiki shi ne “saboda matsalolin lafiyya” da suka fara shafar aikinsa.
Shugaba Tinubu ya karɓi murabus ɗin tare da gode masa bisa hidimar da ya yi wa ƙasa tun daga lokacin da aka naɗa shi a ranar 21 ga Agusta, 2023. Rahotanni sun nuna cewa fadar shugaban ƙasa na shirin sanar da majalisar dattawa sunan wanda zai maye gurbin Badaru nan da ƙarshen mako.
Badaru, mai shekaru 63, ya shugabanci jihar Jigawa tsakanin 2015 zuwa 2023 kafin naɗin nasa a matsayin minista.
Murabus ɗin ya zo ne a daidai lokacin da Shugaba Tinubu ya ayyana dokar ta ɓaci kan tsaro a faɗin kasar, sannan ana sa ran nan gaba za a fayyace tsare-tsaren da gwamnati za ta bi domin magance matsalolin tsaro.
Wannan ci gaban ya jawo ce-ce-ku-ce a fagen siyasa da tsaro, ganin muhimmancin kujerar ministan tsaro a irin wannan lokaci mai sarƙaƙiya.
Ga masu son bada talla ko shawarwari a kira wannan lambar +2348032077835
Domin samun sauran shirye-shirye Alfijir labarai/Alfijir news ku biyo mu ta nan 👇
https://twitter.com/Musabestseller?s=09
https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165
https://www.threads.net/@alfijirlabarai
https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12
https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag
Alfijir labarai Alfijir News Whatsapp Group 👇👇
https://chat.whatsapp.com/H5oBRaZBdCVIyOTIV5eMfb?mode=ac_t