Yadda Aka Yi Jana’izar Surukar Tsohon Shugaban Najeriya Buhari A Zariya

FB IMG 1719820569739

An yi jana’izar matar surukin tsohon shugaban kasa Muhammadu Buhari, Alhaji Muhammad Sani Sha’abban.

A ranar Lahadi aka yi jana’izar Hajiya Bilkisu a unguwar GRA da ke Zariya.

Marigayiya Hajiya Bilkisu Sha’aban wadda ita ce ta biyu a gidan mijinta, ta rasu ne a ranar Asabar a wani asibiti da ke Abuja bayan doguwar jinya.

’Yar shekara 52, Marigayiya Hajiya Bilkisu ta bar yara uku da mijinta, Alhaji Sani Sha’aban.

Marigayiyar ’ya ce ga fitaccen tsohon editan jaridar New Nigeria, Kaduna, Marigayi Alhaji Usman Mairiga.

Mijinta, shi ne Danburan din  Zazzau kuma tsohon dan takarar gwamnan jihar Kaduna, Alhaji Sani Mahmud Sha’aban.

Cikin wanda suka halarci jana’izar, har da Mataimakin Shugaban Jam’iyyar APC na Kasa mai kula da Shiyyar Arewa maso Yamma, Honorabul Garba Mohammed Babawo.

Tuni dai aka kai ta makwancin ta a makabartar Dakace da ke Zariya a ranar Lahadi.

Aminiya

Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a

https://twitter.com/Musabestseller?s=09

https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165

https://www.threads.net/@alfijirlabarai

https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12

https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag

Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijr Labarai 👇👇

https://chat.whatsapp.com/ELQRQyq1zGn7zpAVP8DwNj

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *