Yadda Cincirindon Jama’a Suka Yi Cikar Kwari A Katsina Yayin Mauludin Sheikh Ibrahim Niasse Karo Na 40.

IMG 20260118 WA0204

Fiye da Musulmi miliyan uku daga sassa daban-daban na Najeriya da wasu ƙasashen Afirka ne sukayi tsinke a jihar Katsina domin gudanar da bikin Mauludin (ranar haihuwa) marigayi jagoran addinin Tijjaniyya, Sheikh Ibrahim Niasse.

Jaridar Alfijir Labarai Ta Rawaito an gudanar da taron addinin na tsawon mako guda a Filin Wasanni na MUHAMMAD Dikko, Katsina, kuma ƙungiyar Majma’u Ahbab Niasse ce ta shirya shi. Taron ya samu halartar manyan malamai na Musulunci, sarakunan gargajiya, da dubban mabiya ɗariƙar Tijjaniyya daga jihohi 36 na Najeriya da kuma ƙasashen Yammacin Afirka makwabta.

Da yake jawabi a wajen taron, Shugaban Majma’u Ahbab Niasse, Sheikh Ahmad Tijjani Sani Auwal, ya bayyana cewa bikin Mauludin na shekarar 2026 ya kasance na cika shekara 40 ana gudanar da wannan taro a duk shekara.

Ya ce an shirya taron ne domin girmama rayuwa da koyarwar Sheikh Ibrahim Niasse, tare da yin addu’o’i na neman zaman lafiya, haɗin kai da bunƙasar tattalin arziki a Jihar Katsina da kuma Najeriya baki ɗaya.

Sheikh Auwal, wanda kuma shi ne Kwamishina a Ma’aikatar Harkokin Addini ta Jihar Kano, ya bayyana cewa Katsina na karɓar bakuncin Mauludin ne karo na uku, bayan an taba gudanar da shi a jihar a shekarar 2002 da 2016. Ya ƙara da cewa jihohi irin su Zamfara, Sokoto da Kebbi ma sun taɓa karɓar bakuncin irin wannan biki a baya.

Ya yaba wa Gwamnatin Jihar Katsina bisa samar da yanayi na zaman lafiya da kwanciyar hankali yayin taron, tare da yin addu’ar ɗorewar zaman lafiya da haɗin kai a jihar da ƙasar gaba ɗaya.

A nasa jawabin, Sarkin Kano, Khalifa Muhammadu Sanusi II, ya yi kira ga mabiya ɗariƙar Tijjaniyya da kuma al’ummar Musulmi baki ɗaya da su ƙara haɗin kai. Yana mai jaddada rawar da Sheikh Ibrahim Niasse ya taka wajen yaɗa Musulunci a faɗin Afirka, inda ya bayyana shi a matsayin babban malami mai tasiri wanda tarihinsa ya wuce iyakokin ƙasashe.

Tunda Farko, A jawaban da ya gabatar, Gwamnan Jihar Katsina, Dakta Dikko Umaru Radda, ya nuna godiya ga masu shirya taron bisa zaɓar Katsina a matsayin jihar da ta karɓi bakunci. Ya tabbatar da aniyar gwamnatinsa na ci gaba da tallafa wa harkokin addini da ke inganta zaman lafiya, haɗin kai da daidaituwar al’umma, tare da roƙon a ci gaba da yi wa Najeriya addu’a.

Manyan baki daga Najeriya da ƙasashen Yammacin Afirka sun halarci taron, ciki har da wakilan Babban Sakatare na Kungiyar Haɗin Kan Kasashen Musulmi (OIC), da kuma Khalifa Sheikh Mahi Sheikh Ibrahim Niasse, wanda Muhammad Qurash Sheikh Ibrahim Niasse daga Senegal ya wakilta.

An fara gudanar da Mauludin ne a ranar Lahadi, inda ya ɗauki tsawon kwana bakwai, sannan aka rufe shi a ranar Asabar da karatun Alƙur’ani, addu’o’i, wa’azuzzuka da tarukan ilimi, duk suna bayyana rayuwa, koyarwa da gado mai ɗorewa na shahararren jagoran Tijjaniyya, Sheikh Ibrahim Niasse.

Ga masu son bada talla ko shawarwari a kira wannan lambar +2348032077835

Domin samun sauran shirye-shirye Alfijir labarai/Alfijir news ku biyo mu ta nan 👇

https://twitter.com/Musabestseller?s=09

https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165

https://www.threads.net/@alfijirlabarai

https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12

https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag

Alfijir labarai Alfijir News Whatsapp Group 👇👇

https://chat.whatsapp.com/H5oBRaZBdCVIyOTIV5eMfb?mode=ac_t

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *