Yadda Wata Uwa Ta Jefo Jaririn Da ta Haifa Daga Saman Bene

IMG 20250224 WA0029

Daga Aminu Bala Madobi

Alfijir Labarai ta rawaito wani jariri ya mutu har lahira a birnin Paris a ranar litinin bayan da mahaifiyarsa ‘yar shekara 18 ‘yar kasar Amurka ta jefo shi daga nisan benan otal.

A cewar masu gabatar da kara na Faransa da wata majiyar ‘yan sanda, ta jefo jaririn daga tagar bene na biyu na wani otal da ke unguwar ta 20 a gabashin birnin Paris, in ji ofishin mai gabatar da kara.

“An baiwa jaririn kulawar gaggawa amma Kash bai tsira ba rai yayi halin sa,” in ji masu gabatar da kara.

Majiyar ‘yan sandan ta ce an sanar da ‘yan sanda bayan an gano wani jariri sanye da riga, wanda har yanzu sauran kayan dake sanye da jikin jaririn ke makale a gaban otal din.

Mahaifiyar ‘yar shekara 18, ‘yar asalin kasar Amurka, ta haihu a wani daki da ke hawa na biyu na otal din, sannan ta jefar da yaron ta ta taga, kamar yadda majiyar ta bayyana.

Jami’an tsaron Faransa sun ce sun kaddamar da binciken kisan kai, inda suka kara da cewa matashiyar – wacce “ta kasance cikin rukunin Dalibai matasan da ke balaguro na karatu a Turai” – tuni aka tsare ta.

Jami’an sun kara da cewa matashiyar tayi hakane domin dakile barazanar lamarin hana daukar ciki.”

An kai mahaifiyar asibiti inda za a cigaba da yi mata magani bayan haihuwar ta, kamar yadda ofishin mai gabatar da kara ya ruwaito.

Majiyar Paris Match, ta ba da rahoton cewa mahaifiyar yaron na tafiya tafiya zuwa Paris tare da wasu ayarin dalibai daga Amurka.

Domin samun sauran shirye-shiryen  Alfijir labarai/Alfijir news follow here  👇

https://twitter.com/Musabestseller?s=09

https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165

https://www.threads.net/@alfijirlabarai

https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12

https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag

Alfijir labarai Alfijir News Whatsapp Group 👇👇

https://chat.whatsapp.com/IqPyC2oGzdQ9NudcMXFqHZ

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *