Yadda Yan Adawa Suka Hana Gwamnan Kano Sakat Tsawon Shekara Daya – Kwankwaso

FB IMG 1717881919214

Engr Dr, Rabi’u Musa Kwankwaso, ya zargi wasu ‘yan adawa a Kano da rikita gwamnati na tsawon shekara guda.

Alfijir labarai ta ruwaito Kwankwaso ya bayyana hakan ne lokacin da yake jawabi a wajen taron farfado da harkokin ilimi a jihar Kano.

“Bari in fara da taya Abba Kabir Yusuf murnar wannan rana mai cike da tarihi, ranar da gwamna ke ayyana dokar ta-baci kan ilimi. Muna so su sani cewa gwamnan yana aiki tun daga ranar farko da ya zama gwamnan jihar Kano. In ji Kwankwaso.

Duk da cewa gwamnan ya gamu da kalubale a shekararsa ta farko a gwamnati, jim kadan bayan ya ci zabensa, maƙiyan jihar Kano suka kai shi kotu ta farko, suka tafi har kotun daukaka kara har zuwa Kotun Koli.

“Hatta makiya sun san cewa shi ya ci zaɓen sa, Amma su kai ta kokarin sai sun kwace masa kujerar sa ta karfin tsiya kawai, saboda sun yi imanin cewa suna da gwamnatin tarayya . Duk da haka gwamnan yana aiki, amma kuma yana ta gamuwa da cikas amma bai daina aiki ba.

“A gaskiya wannan ya tuna min halin da muke ciki a wa’adina na biyu bayan watanni biyu da rantsar da ni a matsayin gwamna, mun sha fuskanci hare-haren Boko Haram a masallatai, ana kai hare-hare a kasuwanni, ofisoshin ‘yan sanda, makarantu , amma duk da haka sai da muka mai da hankali muka ga mun yi nasara.”

Daily Trust

Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a

https://twitter.com/Musabestseller?s=09

https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165

https://www.threads.net/@alfijirlabarai

https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12

https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag

Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijr Labarai 👇👇

https://chat.whatsapp.com/ELQRQyq1zGn7zpAVP8DwNj

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *