Yan Sanda Sun Kama Matan Dake Kaiwa ’Yan Bindiga Karuwai

 Rundunar ‘yan sandan Najeriya ta kama wasu mata da suka kware wajen Taimakawa ‘yan fashi da kuma kai musu Mata don holewa. 

Best Seller Channel 

Best Seller Channel 

Kakakin hukumar Yan sandan Najeriya , Frank Mba, ya bayyana cewar, dangane da ayyukan wadanda ake zargin, yayin da daya daga cikin wadanda aka kama ta samu ganawa da su a yayin holin nasu. 

Best seller channel ta rawaito MBA, na cewar rundunar ‘yan sandan Najeriya ba za ta yi kasa a gwiwa ba wajen yakar ‘yan ta’adda da masu hada kai dasu a ko Ina suke a fadin kasar nan. 

A kwanakin baya ne aka kama wasu mata a jihar Kaduna bisa laifin hada baki da ‘yan fashi da kuma taimaka musu wajen aikata laifuka. 

Best Seller Channel 

Da yake ba da cikakken bayani, Frank Mba ya ce, “Wadancan mutanen ’yan asalin garin Zariya ne na jihar Kaduna, suna aiki da wani gungun ‘yan bindiga da suka yi kaurin suna a wani dajin da ke jihar Kaduna, wadanda ake zargin suna taimaka wa ‘yan bindigar ne ta hanyar sanya ido kan wuraren da za a kai hari da kuma sanar da ‘yan fashin da ke cikin daji. 

Wadanda ake zargin ‘suna aiki da yan fashin tare da taimaka musu wajen siyan kayan abinci da magunguna da  kuma baiwa ‘yan fashin mata don jin Dadi. 

Daya daga cikin wadanda ake zargin mai suna Mariam Abubakar tana da saurayi da kanne a sansanin ‘yan fashin,

 Mariam ta kuma gabatar da ‘yan mata a sansanin ‘yan fashin don more rayuwarsa. 

Best Seller Channel 

Da take karin bayani tace ‘Yan fashin, wani lokacin su kan kai ga neman kudin fansa kafin su sako irin wadannan ‘yan matan. 

Frank Mba ya kara da cewa muna kira ga shugabannin al’umma da iyaye da su saka Ido kan motsin al umma da yin aiki da jami’an tsaro a kowane lokaci. 

Slide Up
x