Zan Yiwa Atiku Ritaya A Siyasa, Na Siya Masa Awaki Kaji da Tumaki Yayi Kiwo – Shettima

Mataimakin shugaban kasar Najeriya Kashim Shettima ya ce zai yiwa dan takarar shugaban kasa a jam’iyyar PDP a zaben 2023 Atiku Abubakar ritaya a siyasa zuwa mahaifarsa, Fombina, sannan ya saya masa dabbobi domin ya yi kiwo.

Alfijir Labarai ta rawaito Mataimakin Shugaban kasar Najeriya Kashim Shettima ya bayyana haka ne a lokacin da yake zantawa da manema labarai bayan da kotun sauraron kararrakin zaben shugaban kasa ta tabbatar da nasarar da Bola Tinubu ya samu a kotun daukaka kara a ranar Laraba.

Bayan ya bayyana gamsuwarsa da hukuncin kotun da kuma yin kira ga abokan gaba da su hada kai da shi.

Shettima, tsohon Sanata kuma tsohon gwamnan jihar Borno ya ce, “Mun wuce matakin siyasa. Yanzu, muna cikin harkar mulki.”

Duk wanda ya san zamantakewa da al’adu tsakanin Fulani da Kanuri a arewa zai san cewa ina da ’yancin yi masa duk wani zagi kuma ya hakura.

“Ba za mu yiwa Atiku ritaya zuwa Dubai ko Morocco ba.

Zan yi masa ritaya zuwa Fombina sannan na sayo masa akuyoyi, kaji, da leda domin ya yi kwanakinsa yana kiwon shanu.

Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a

https://twitter.com/Musabestseller?s=09

https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165

https://www.threads.net/@musa_bestseller

https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12

Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijir Labarai  👇

https://chat.whatsapp.com/FNim39ly65N2CzcTt8FgWb

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *