
Alfijr ta rawaito Jam’iyyar New Nigeria Peoples Party (NNPP) ta zargi gwamnatin jihar Kano da yi wa sabuwar gwamnati zagon kasa a jihar.
Da yake jawabi a taron manema labarai a ranar Juma’a, shugaban kwamitin rikon kwarya na gwamnan NNPP, Dr. Abdullahi Baffa Bichi, ya yi zargin cewa da gangan gwamnatin Abdullahi Umar Ganduje ke zagon kasa ta ware wa jam’iyyar NNPP kujeru uku kacal a kwamitin da suka gabatar.
“Muna kallon wannan a matsayin wani yunƙuri ne da gangan na lalata canjin sabuwar gwamnati a jihar,” in ji Bichi.
“Al’ummar Jihar Kano babu abin da suka saka ido, sai dai a samu sauyi cikin kwanciyar hankali da zai kara zurfafa dimokaradiyya a jihar.”
Ya ce gwamnatin mai barin gado ta bukaci su bayar da sunayen mutane uku da za su shiga cikin kwamitin gwamnati, abin da suka ga bai dace ba.

“Gwamnati mai barin gado tana gabatar da wani kwamiti wanda ke da kashi 82 cikin 100 na mambobi (mambobi 14) kuma suna neman gwamnati mai jiran gado ta gabatar da kashi 18 cikin 100 kawai (mambobi uku),” inji shi.
Bichi ya bayyana cewa babban abin da ake ta cece-kuce a kai shi ne ka’ida, domin ba jam’iyya daya ba ce kuma ba su da manufa daya da dabi’u daya.
A cewarsa, “Akwai sauyi iri uku: daya, daga gwamnati daya zuwa kanta; biyu, daga wannan gwamnati zuwa wata gwamnatin jam’iyyar siyasa daya; da uku, daga wannan gwamnati zuwa wata gwamnatin wata jam’iyyar siyasa daban.’’
“A na uku, inda ake da jam’iyyun siyasa daban-daban, an kafa kwamitin mika mulki na daban ga gwamnati mai zuwa.”
Sai dai shugaban kwamitin rikon kwarya na NNPP ya bayyana shirin yin hulda da sakatarorin dindindin da daraktoci domin tabbatar da mika mulki ga gwamnati ba tare da wata matsala ba.
Shugaban kwamitin mika mulki na NNPP ya yi kira ga Gwamna Ganduje da ya ba da hadin kai don tabbatar da mika mulki cikin sauki.
“Muna kira ga Gwamna Ganduje da ya sanya maslahar al’ummar Jihar Kano a gaba, ya kuma hada kai da mu wajen ganin an samu sauyi ba tare da wata matsala ba.
“Mun kuduri aniyar yin aiki don ganin an mika mulki cikin sauki, kuma muna fatan gwamnatin mai barin gado za ta yi hakan,” in ji Bichi.
Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a
Facebook. Alfijr Labarai
YouTube. Best Seller Channel
Twitter. @Musabestseller
Instagram. @musa_bestseller
Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijr Labarai 👇
https://chat.whatsapp.com/G1wNveF9mGU7jec5mWhFvZ