
Alfijr ta rawaito wata Mummunar Gobara ta kama a fadar babban basarake a jihar Oyo mai riƙe da sarautar Ooni na Ife.
Wasu ganau sun bayyana ana tunanin gobarar ta kama ne a dalilin wutar lantarki da ta zo da ƙarfi.
Wani ɓangare na fadar ya kama da wuta ne da misalin ƙarfe 11:30 na daren ranar Juma’a, 28 ga watan Afirilun 2023, jim kaɗan bayan kayan wutar lantarkin fadar sun yi bindiga.
Sai da ƴan kwana-kwana da dogarawan fadar da mutanen gari suka yi da gaske sannann suka samu nasarar kashe gobarar.

Kakakin fadar, Otunba Moses Olafare, ya tabbbatar da cewa tuni har an shawo kan matsalar.
Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a
Facebook. Alfijr Labarai
YouTube. Best Seller Channel
Twitter. @Musabestseller
Instagram. @musa_bestseller
Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijr Labarai 👇
https://chat.whatsapp.com/G1wNveF9mGU7jec5mWhFvZ