Dogarin Zababben Gwamnan Kano Ya Rasa Ransa A Hatsarin Mota

📸 Kwankwasiyya Reporters


Alfijr ta rawaito ranar Asabar din da ta gabata ne wani Haɗarin mota yayi sanadiyar rayuwar babban dogarin zababben gwamnan jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, Abdulrahman Gambo, a hanyar garin Bichi.

Wani ganau ya bayyana cewa abokin aikin marigayi Gambo, mai suna Cena ya tsira daga hatsarin.

Majiyar ta yi nuni da cewa a halin yanzu Cena yana wata cibiyar lafiya yana karɓar kulawar likitoci.

Rahotanni sun bayyana cewa, manyan jami’an tsaron sun je ne domin halartar wani bikin daurin aure a garin Bichi, yayin da suke kan hanyarsu ta komawa Kano, motar tasu “tai ta yawo akan babbar hanyar, inda tayi hatsari mutum daya ya mutu, yayin da daya kuma ya tsira da ransa”.

An yi jana’izar marigayi Gambo a Kano kamar yadda Shari’a ta tanada.

Zababben gwamnan, Alhaji Yusuf ya ce “Na yi matukar bakin ciki da samun labarin rasuwar Abdulrahman Gambo a hadarin mota. ”

Sai dai ya bayyana cewa “Abdulrahman, mutum ne mai kishi da aminci a cikin tawagar tawa. Kuma, ni da duk wanda ke kusa da shi za mu yi kewarsa”.

Don haka ya roki Allah da ya ba shi hutu na dindindin, ya gafarta masa kura kuransa.

Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a

Facebook.   Alfijr Labarai
YouTube.     Best Seller Channel
Twitter.        @Musabestseller
Instagram.  @musa_bestseller

Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijr Labarai 👇

https://chat.whatsapp.com/G1wNveF9mGU7jec5mWhFvZ

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *