Alfijr ta rawaito hukumar bautar ƙasa ta Nijeriya NYSC ta ja hankulan jama’a game da wani labari da ke ci gaba da yawo a yanar gizo inda suka yi zargin cewa wasu ‘yan kungiyar mata a sansanin NYSC Permanent Orientation Camp da ke Yikpata a jihar Kwara sun kama masu amfani da al aurar maza.
Ina so in bayyana dalla-dalla cewa irin wannan tabarbarewar dabi’a ba ta taba faruwa a sansanin Yikpata ba, domin wannan rahoto ya yi nuni da tunanin marubucin don kawai ya jawo hankalin kafafen yada labarai. In ji sanarwar.
Hakazalika ina ba jama’a shawara, musamman masu ruwa da tsaki na wannan tsari da su yi watsi da labaran karya gaba daya, wanda ba shi da tushe kuma ba shi da asali wanda zai saka mutane a rudani.

Jama’a na sane da cewa NYSC na murnar zagayowar ranar Jubilee na Zinare da manufar karfafa dimbin nasarorin da ta samu a cikin shekaru 50 da suka gabata na mayar da matasan Najeriya da suka kammala karatun digiri a matsayin ‘yan kasa masu nagarta da kuma abin koyi.
Har ila yau, ina sake jaddada cewa NYSC jihar Kwara za ta ci gaba da aiwatar da manufofin wannan tsari don kara sanya matasanmu amintattu da shugabannin da suka cancanta wajen gina kasa.
Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a
Facebook. Alfijr Labarai
YouTube. Best Seller Channel
Twitter. @Musabestseller
Instagram. @musa_bestseller
Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijr Labarai 👇
https://chat.whatsapp.com/G1wNveF9mGU7jec5mWhFvZ
mashaAllah