Shugaba Buhari Ya Nada Mace Ta Farko Akanta Janar Ta Tarayya

Alfijr ta rawaito Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya amince da nadin Oluwatoyin Sakirat Madein a matsayin sabuwar Akanta Janar na Tarayya.

Hakan na kunshe ne a cikin wata sanarwa mai dauke da sa hannun daraktan sadarwa na shugaban kasa, Mohammed Ahmed a ranar Juma’a.

Sanarwar ta ce Madein, tare da wasu ‘yan takara 19 an tantance su domin neman mukamin a watan Janairu.

“Shugaban kasa, Muhammadu Buhari, ya amince da nadin Dakta (Mrs) Oluwatoyin Sakirat Madein, a matsayin babban Akanta-Janar na Tarayya bayan nasarar gudanar da zaben cike gurbin da ake da shi,” in ji sanarwar.

“Shugaban ma’aikatan gwamnatin tarayya. Dr. Folasade Yemi-Esan, CFR ta bayyana haka ne a yau Juma’a 19 ga watan Mayu 2023 a Abuja, inda ta kara da cewa nadin zai fara aiki daga ranar Alhamis 18 ga watan Mayu 2023.’’

Ta ce sabuwar wanda aka nada zata ci gaba da aiki cikin gaggawa.

‘’Kafin wannan nadin, ta yi aiki a matsayin Darakta, Kudi da Akanta, ofishin shugaban ma’aikatan gwamnatin tarayya. a Management Finance daga Walden University, Minnesota, Amurka kuma za ta zama mace ta farko da ta fara zama wannan ofishin a Najeriya.

Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a

Facebook. Alfijr Labarai
YouTube. Best Seller Channel
Twitter. @Musabestseller
Instagram. @musa_bestseller

Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijr Labarai 👇

https://chat.whatsapp.com/G1wNveF9mGU7jec5mWhFvZ

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *