
Alfijr ta rawaito Ministan Harkokin Sufurin Jiragen Sama, Hadi Sirika, ya tsaya kai da fata cewa jirgin Nigeria Air mallakin Gwamnatin Tarayya zai fara shawagi kafin Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya bar mulki.
A cewar Ministan, jirgin zai iso Najeriya ranar Juma’a, kwana uku kafin Buhari ya bar mulkin.

A baya dai Ministan ya sha fadin cewa komai ya kammala domin fara jigila da jirgin kafin karewar wa’adin Buhari.
Ya bayyana hakan ne yayin wata tattaunawarsa da gidan talabijin na Channels a ranar Laraba, wacce wakilinmu ya kalla.
“Dangane da batun jirgin Nigeria Air, zai iso kasar nan ranar Juma’a a wani bangare na shirye-shiryen fara aikinsa.

“A ranar za mu kaddamar da jirgin wanda ke dauke da launin tutar Najeriya, kafin mu ci gaba da kwaso ragowar jiragen,” in ji shi.
Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a
Facebook. Alfijr Labarai
YouTube. Best Seller Channel
Twitter. @Musabestseller
Instagram. @musa_bestseller
Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijr Labarai 👇
https://chat.whatsapp.com/GdLiqZyHuSz5NhjdGoGRGZ