Kotu Tayi Watsi Da Karar PDP Ta Kuma Tabbatar Da Nasarar Tinubu

Alfijr ta rawaito Kotun koli a Najeriya tayi watsi da ƙarar da jam’iyyar PDP ta shigar gaban ta, inda take buƙatar kotun ta tabbatar da rashin nasarar Tinubu da Shatiima na Jam’iyyar APC.

Alkalan kurun mai mutane 5 da suka jagoranci yanke hukuncin a Juma’a, sun bayyana cewa jamiyyar PDP bata da hujjojin da zata dogara da su wajen karar.

Alkalan sun ce jam’iyyar PDP ba mamba bace a jam’iyyar APC, a don haka bata da wata dama da zata iya tafiyar da wannan karar.

PDP dai ta dogara da sashi na 29 (1) da sashi na 33, 35 da 84 (1)(2) na dokar hukumar zabe ta 2022, wajen shigar da karar.

Jam’iyyar dai ta kalubalanci yadda aka zabi Kashim Shatima daga jihar Borno domin tsayawa Tinubu a matsayin mataimaki, suna masu bayyana hakan da cewa ya sauka a layi.

Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu aFacebook. Alfijr Labarai YouTube. Best Seller ChannelTwitter. @MusabestsellerInstagram. @musa_bestsellerKo a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijr Labarai 👇https://chat.whatsapp.com/GdLiqZyHuSz5NhjdGoGRGZ

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *