Alfijr ta rawaito Babbar Kotun shari’ar addinin musulnci dake zaman ta a Unguwar Danbare karamar hukumar Kumbotso a jihar Kano, ta dage ci gaba da sauraran shari’ar da wani dan kasuwa da ya shigar da Mawaƙi Dauda Kahutu Rarara.

Dan kasuwar dai ya shigar da Rarara kara ne, bisa kin biyansa wasu kudaden kasuwanci sama da naira miliyan 10.
Dan kasuwar mai suna Muhammad Ma’aji , shi ne ya Yi karar Mawaƙin a gaban Kotun bayan ya Gaza cika alkawarin da ya daukar masa.
Kunshin tuhumar dai na zargin Rarara ya karbi wayoyin salula a wajen dan kasuwar inda yake raba Su ga jama’a.
Haka zalika akwai kuma kudin Data da katin TV da yake sanya wa Iyalan mawakin da yaransa.
Wadanda kudin suka taru har Suka Kai yawan da yake rokon Kotun ta karba masa hakkinsa.
To sai dai an dage zaman a yau juma’a ne sakamakon Alkalan kotunan suna gudanar da taro duk karshen wata.
Yanzu haka dai za a Ci gaba da sauraran shari’ar zuwa ranar 5 ga watan Yuni 2023.
Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a
Facebook. Alfijr Labarai
YouTube. Best Seller Channel
Twitter. @Musabestseller
Instagram. @musa_bestseller
Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijr Labarai 👇