Ya Kamata A Ƙirƙirar wa Tsoffin Matan Shugabannin Ƙasa Wani Gata Bayan Barin Mulki – Aisha Buhari

Alfijr ta rawaito mai dakin shugaban kasa mai barin gado, Aisha Buhari, ta yi kira da a yi amfani da wasu gata irin na samar da ababen hawa, daukar nauyin tafiye-tafiye na neman lafiya da bayar da wasu alawus-alawus da ake baiwa tsoffin shugabannin kasar, ga matan shugabannin kasa.

Buhari ta ce matan shugaban kasa sun cancanci wannan gata kamar yadda mazajensu ko Shugabanni suke a ofis da kuma barin ofis rashin aiki saboda idan matsin lamba ya zo, ba wanda yake son sanin ceww ko kun fita daga Villa ko a’a.

Aisha Buhari ta yi magana ne a wajen kaddamar da wani littafi a Abuja wanda shugabar kungiyar matan jami’an tsaro da ‘yan sanda (DEPOWA), Misis Vickie Anwuli Irabor ta rubuta mai suna, “Rayuwar matar Soja”.

Da ta ke bayyana dalilin da ya sa za a kara wa matan shugabannin kasa wannan gata, Misis Buhari ta ce, “Na auri mijina a matsayin matar tsohon shugaban kasa. Zan tafi nan da ‘yan kwanaki a matsayin matar tsohon shugaban kasa karo na biyu.

“Ya kamata su dauke mu a matsayin matan tsohon shugaban kasa. Kamata ya yi su hada da matan shugaban kasa, su ba mu wasu gata da muka cancanta a matsayinmu na matan shugaban kasa, ba wai tsoffin shugabannin kasa kadai ba”.

Daily Nigerian

Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a

Facebook.   Alfijr Labarai
YouTube.     Best Seller Channel
Twitter.        @Musabestseller
Instagram.  @musa_bestseller

Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijr Labarai 👇

https://chat.whatsapp.com/GdLiqZyHuSz5NhjdGoGRGZ

One Reply to “Ya Kamata A Ƙirƙirar wa Tsoffin Matan Shugabannin Ƙasa Wani Gata Bayan Barin Mulki – Aisha Buhari”

  1. Ahakanma abunda kuka yimana bamu yafeba wllh barekuma harmugoyi bayan karamuku wani gana namusamman akasarnan akwai wadanda suka fiku Babu abunda akayiwa matayansu misali malaman makaranta likitoci dakuma jami an tsaro d.s Mai akayiwa matayansu alokacinma dasuke kan aikinsu barema Kuma insun Gama aiki yau kwanan mijinki nawa bebawa malam jami o I hakkinsuba duk bakuyi magana akan abasuba kosu bamutanebane inaga kwanannan likitoci masusan kwarewar aiki suka Gama yajin aiki maikuka yimusu kosu bamutanebane saidai kezakubar mulki shine kikeyin wannan maganan hmmmmmm Allah mai iko to muna jiranki kudawo cikinmu kufara ganin yadda kuka zalinci talakawan kasa tunkafinmu Kuma muje inda Allah zai bayyanawa kowa hakkinsa nagaskiya dahakan nema akullin muke cewa mudaku saidai Allah yabimana hakkinmu domin bazamu yafeba har abada indai kuncutar damu Allah yayimana sakayya.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *