
Alfijr ta rawaito an dakatar da wani jami’in gwamnatin India bayan ya bayar da umarnin janye ruwan wani dam domin gano wayarsa ta salula.
An shafe kwana uku ana janye miliyoyin lita na ruwan dam ɗin bayan wayar Rajesh Vishwas ta faɗa ciki a lokacin da yake ɗaukar hoto (selfi)

Lokacin da aka gano wayar, ta sha ruwa ba za ta yi aiki ba.
Mista Vishwas ya yi ikirarin cewa wayar na ƙunshe da muhimman bayanai na gwamnati wanda ya zama wajibi a gano ta, amma an zarge shi da yin sakaci.
Wayar jami’in ƙirar Samsung ce da aka bayyana darajarta ta kai dala 1,200, kuma ta faɗa ne dam din Kherkatta a jihar Chhattisgarh da ke tsakiyar India a ranar Lahadi.
Bayan masu ninkaya a yankin sun gaza gano wayar, jami’in ya yi hayar masu amfani da injin domin janye ruwan, kamar yadda ya bayyana a cikin wani bidiyo da kafofin yadda labaran India suka bayyana.
An dakatar da shi yanzu haka, kuma hukumomi sun ce ruwa muhimmin abu ne da bai kamata a yi hasara ba, kamar yadda wata jami’a Priyanka Shukla a yankin Kanker ta shaida wa wata jaridar ƙasar.
BBC Hausa
Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a
Facebook. Alfijr Labarai
YouTube. Best Seller Channel
Twitter. @Musabestseller
Instagram. @musa_bestseller
Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijr Labarai 👇
https://chat.whatsapp.com/GdLiqZyHuSz5NhjdGoGRGZ