Zaɓaɓɓen Gwamnan Kano Ya Bayyana Kadarorinsa kwanaki kadan Kafin karɓar mulki

Alfijr ta rawaito zababben Gwamnan Kano mai jiran gado Abba Kabir Yusuf ya ayyana kaɗarorin da ya mallaka ga hukumar ɗa’ar ma’aikata.

 Sanarwar da ofishin gwamnan mai jiran gado ya fitar a ranar Juma’a ta ce Abba Kabir Yusuf ya gabatar da kansa ga ofishin hukumar ɗa’ar ma’aikata da ke Kano tare da miƙa fom da ya cike na ƙadarorinsa.

“Na cika sharuɗɗan da kundin tsarin mulki ya gindaya na ayyana ƙadarorin da na mallaka kafin rantsar da ni a 29 ga Mayu,” in ji sanarwar.

Abba Kabir Yusuf ya kuma sanar da matakinsa a shafinsa na Twitter

Hakazalika ya kuma bayyana cewa dukkanin jami’an da za su yi aiki a gwamnatinsa da suka ƙunshi har da muƙaman siyasa sai sun bayyana ƙadarorinsu kamar yadda doka ta tanada.

Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a

Facebook.   Alfijr Labarai
YouTube.     Best Seller Channel
Twitter.        @Musabestseller
Instagram.  @musa_bestseller

Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijr Labarai 👇

https://chat.whatsapp.com/GdLiqZyHuSz5NhjdGoGRGZ

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *