
Alfijr ta rawaito Gwamnatin Jihar Kano ta ce daga yanzu kwacen waya ya zama daidai da fashi da makami a Jihar.
Hakazalika duk wanda aka kama hukunci iri daya za a rika yanke masa da dan fashi da makami.
Kwamishinan Yada Labarai da Al’amuran Cikin Gida na Jihar mai barin gado, Malam Muhammad Garba ne ya tabbatar da hakan a wata sanarwa da safiya Asabar.

Ya ce daukar matakin ya biyo bayan taro Majalisar tsaro ta Jihar a zamantan na bankwana, wacce Gwamna mai barin gado, Abdullahi Umar Ganduje ya jagoranta.
A cewarsa, yawan faruwar kwacen waya a jihar a ’yan kwanakin nan abin damuwa ne wanda kuma ake bukatar tsatstsauran mataki kafin a iya dakile shi.
Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu aFacebook. Alfijr Labarai YouTube. Best Seller ChannelTwitter. @MusabestsellerInstagram. @musa_bestsellerKo a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijr Labarai 👇https://chat.whatsapp.com/GdLiqZyHuSz5NhjdGoGRGZ