Gwamnatin Neja Ta Bayar Da Umarnin Rusa Gidan Mai

Alfijr ta rawaito Mohammed Umaru Bago ya soke takardar shaidar zama gidan mai tare da bayar da umarnin rushe shi a Minna babban birnin jihar.

Gwamnan ya ba da umarnin ne a lokacin da ya ziyarci gidan mai da ke Ketaren Gwari, cikin babban birnin Minna.

A cewarsa, ginin ya sabawa doka, kuma wurin da yake bai dace ga al’ummar yankin ba, inda ya ce tun da farko ya bukaci masu gidan man su daina aiki.

Ya ce: “Muna da rahoton tsarin da aka yi ba bisa ka’ida ba, kuma na roki hukumar raya birane da ta hana su aiki, amma sun ci gaba, don haka muka soke takardar C of O daga yau, kuma za mu sanya masa lamba don rugujewa.”

Bago ya kara da tabbatarwa: “Ba a gina shi a tsakanin mutane ba, yana da hadari ga rayuwarsu, kuma ba abin yarda ba ne.”

Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a

Facebook. Alfijr Labarai
YouTube. Best Seller Channel
Twitter. @Musabestseller
Instagram. @musa_bestseller

Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijr Labarai 👇

https://chat.whatsapp.com/GdLiqZyHuSz5NhjdGoGRGZ

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *