Alfijir Labarai ta rawaito Ma’aikatar ilimi ta jihar Kano ta amince da ranar Juma’a 23 ga Yuni, 2023 a matsayin ranar da za a fara hutun Sallah Eid-el Kabir na duk makarantar gwamnati da masu zaman kansu.
Hutun Sallah wanda zai dauki tsawon mako daya wanda zai kare ranar Asabar 1 ga Yuli, 2023, don haka dukkan daliban makarantun kwana za su koma ranar Lahadi 2 ga watan Yuli yayin da wadanda ke makarantun jeka ka dawo za su koma ranar Litinin 3 ga Yuli.
Babban sakataren ma’aikatar, Malam Ahmad Tijjani Abdullahi ya bukaci iyaye/Masu kula da dalibai da daliban makarantun da su tabbatar da bin ka’idojin da aka amince da su na komawa aiki.
Yayin da yake yi masu fatan Barka da bukukuwan Sallah tun da wuri, ya kuma yi kira gare su da su kasance masu amfani ga iyayensu da kuma guje wa yawo da ba dole ba a lokacin hutun Sallah.
Sakataren ya kuma yi gargadin cewa za a dauki matakin ladabtarwa a kan daliban da suka ki bin ka’idar.
Kamar yadda daraktan wayar da kan jama’a na ma’aikatar ilimi ta jihar Kano ya sanar.
Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a
Facebook. Alfijir Labarai
YouTube. Best Seller Channel
Twitter. @Musabestseller
Instagram. @musa_bestseller
Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijir Labarai 👇
https://chat.whatsapp.com/GdLiqZyHuSz5NhjdGoGRGZ
gaskiye hakai yayi sosai