Gwamnan Jihar Kano, Abba Kabir Yusuf ya sake buɗe asibitin yara na mai suna Hasiya Bayero Paediatric Hospital.
Alfijir Labarai ta rawaito yayin jawabin nasa wajen buɗe asibitin, Gwamna Yusuf ya zargi gwamnatin Abdullahi Umar Ganduje da sayar da asibitin, lamarin da ya jefa al’ummar jihar cikin halin wahala.
A cewar sa, hakan ta sanya ya ci alwashin idan dai ya zama gwamnan Kano sai ya ƙwato wa al’umma kayan su.
“Duk da irin rokon da al’umma su ka riƙa yi, amma gwamnatin da ta gaba ta sayar da wannan asibiti. Hakan ya sanya al’umma suka rika shan wahala. Dole su ka riƙa zuwa neman asibitocin yara masu tsada kuma ba lallai suna da ingancin wannan ba.
“Da mu ka ga haka, sai mu ka ci alwashin kwatowa al’umma asibitin su. Yau ga shi mun cika alƙawari. Mu na cikin farin ciki da alfahari da wannan gagarumin aikin,” in ji gwamna Abba.
Ya ce asibitin na ɗauke da wajen gadaje 86, kuma an saka masa kayayyakin aiki na zamani da za a rika kiwon lafiya cikin inganci da sauƙi.
Ya kuma ja kunnen jami’an lafiya na asibitin da su kula da gudanar da ayyukan su, inda ya gargaɗe su a kan yin fashi da latti, inda ya ce “gwamnati ba za ta lamunci sakaci da aiki ba.”
A nashi jawabin, Sarkin Kano, Alhaji Aminu Ado Bayero, ya godewa gwamna Yusuf bisa kokarin da ya yi na sake buɗe asibitin.
Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a
Facebook. Alfijir Labarai
YouTube. Best Seller Channel
Twitter. @Musabestseller
Instagram. @musa_bestseller
Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijir Labarai 👇
https://chat.whatsapp.com/Jmw5CBsPV6H3DbSgnlFUHM