Tirabunal ta kori Gwamna Sule ta kuma ce ɗan takarar PDP ne ya lashe zaɓen Nassarawa
Alfijir Labarai ta rawaito Kotun sauraren kararrakin zaben gwamna da ke zamanta a garin Lafia a jihar Nasarawa ta kori Gwamna mai ci na jihar, Abdullahi Sule tare da bayyana David Ombugadu dan takarar jam’iyyar adawa ta PDP a matsayin wanda aka zaba.
A hukuncin da aka yanke a yau Litinin, biyu daga cikin alkalan sun amince cewa PDP ce ta lashe zaben yayin da alkali daya ya nuna rashin amincewarsa.
Gwamna Sule na jam’iyyar APC, ya nemi sake tsayawa takara a karo na biyu amma ya fuskanci turjiya a lokacin zaben.
Sule ya samu kuri’u dubu 347,209 inda ya doke abokin takarar sa Ombugadu wanda ya samu kuri’u 283,016.
Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a
https://twitter.com/Musabestseller?s=09
https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165
https://www.threads.net/@alfijirlabarai
https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12
https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag
Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijir Labarai 👇
https://chat.whatsapp.com/FNim39ly65N2CzcTt8FgWb