Takaitattun labaran duniya na Alhamis 12/10/2023CE – 27/03/1445AH

best seller i

Daga Baba Usman Gama

Shugaba Bola Tinubu ya naɗa Ola Olukoyede a matsayin sabon shugaban hukumar EFCC.

Saidai Jigo a jam’iyyar APC Daniel Bwala ya zargi Bola Ahmed Tinubu da sabawa dokar kasa wajen nada sabon shugaban da zai jagoranci EFCC.

‘Yan sanda sun cafko wanda da bakinsa ya fadi yadda su ka yi garkuwa da daliban FGC Yauri dake jihar Kebbi a shekarar 2021.

Cutar mashaƙon diphtheria ta kashe mutum 600 a Najeriya.

Ƴan bindiga sun kashe mutum 1,715 a Najeriya cikin wata uku.

NAHCON ta ba maniyyata Aikin Hajjin badi mako 3 su fara biyan kudadensu.

Yan sanda sun kama Wani mahaifi mai shekara 42 a Jihar Legas, bisa zarginsa da shafe tsawon shekara 3 yana yi wa ’yar cikinsa fyade.

Kwamandan Hisbah ta Kano Sheikh Daurawa yace sun shirya tsaf don aurar da mata 1,800, a gobe a Masallatan Juma’a a fadin jihar.

‘Yan sanda sun kama barayin shanu da masu safarar muggan kwayoyi a Jigawa.

Wasu ƴan bindiga sun halaka wani mutum da ya je kai kuɗin fansa a jihar Kaduna.

Jami’an tsaro sun cafke wani matashi da ya hada baki da wasu don yi wa abokinsa fashi a Kano.

Daruruwan mutane ne suka fito zanga zangar nuna goyon bayan Falasdinu a Afirka ta Kudu inda suka zargi Amurka da hannu wajen musgunawar da Isra’ila take yi musu.

Jirgin fasinja mai tarago 21 yi hatsari a Indiya.

An dakatar da jami’in MDD a Congo kan cin zarafi da lalata.

An daure matar tsohon shugaban kasar Gabon Ali Bongo Odimba a gidan yari.

Kungiyar Hamas ta ce ta sako wasu ƴan Isra’ila da take tsare da su.

Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a

https://twitter.com/Musabestseller?s=09

https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165

https://www.threads.net/@alfijirlabarai

https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12

https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag

Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijir Labarai 👇

https://chat.whatsapp.com/K8z1chFesJeCf99QehWJPo

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *