Daga Baba Usman Gama
Kotun Koli ta tabbatar da nasarar Bola Tinubu a matsayin shugaban kasa.
Shugaba Tinubu yace nasarar da ya samu a kotu ta kara mishi karfin gwiwar yi wa ‘yan kasa aiki.
PDP ta ce hukuncin Kotun Koli a kan korafin da ta shigar a kan nasarar zaben Shugaba Tinubu babban abin tayar da hankali ne.
Majalisar dattawa ta tabbatar da naɗin Musa Aliyu a matsayin sabon shugaban hukumar yaki da cin hanci da rashawa mai zaman kanta (ICPC).
Sojoji sun kashe ’yan ta’addan Boko Haram 5 a Yobe.
Dakarun sojoji sun samu gagarumar nasarar cafke wasu miyagun mutum 2 masu safarar makamai ga ƴan ta’adda a Kaduna
An sake kama Abba Kala, daya daga cikin fursunonin nan da ke zaman jiran hukunci kuma ya tsere daga gidan gyaran hali na Katsina.
Faransa zata sanya sojojin ruwanta cikin masu aikin bada agaji a Gaza.
Harin ‘yan bindiga ya kashe mutane fiye da 20 a Amurka.
Firaministan Nijar, ya zargi ECOWAS da rashin adalci a takunkumin da ta ƙaƙaba wa ƙasar bayan hamɓarar da gwamnatin farar hula ta Bazoum Mohamed.
Hamas ta ce an kashe waɗanda ake garkuwa da su 50 da fara luguden wutar Isra’ila.
Koriya ta Arewa ta zargi Isra’ila da ‘aikata munanan laifuka karkashin goyon bayan Amurka.
Shugaban ƙasar Turkiyya ya yi kakkausar suka kan matakin da gwamnatocin ƙasashen Yamma suka ɗauka kan hare-haren da Isra’ila ke kai wa Gaza.
Motocin agaji 12 sun tsallaka zuwa Gaza a yau Alhamis.
Afirka ta Kudu za ta samu rancen dala biliyan 1 daga Bankin Duniya.
Mutanen da suka mutu a hatsarin kwale-kwale a Congo sun kai 54.
Sojojin Sudan da RSF za su ci gaba da tattaunawar zaman lafiya a Jeddah.
Kotu ta samu mutum shida da laifin yunkurin ballewa daga Ghana don kafa kasar ‘Western Togoland.
Hukumar ƙwallon ƙafa ta Italiya ta dakatar ɗan wasan tsakiyar Newcastle da Sandro Tonali na tsawon watanni 10 saboda saɓa ka’idojin caca.
Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a
https://twitter.com/Musabestseller?s=09
https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165
https://www.threads.net/@alfijirlabarai
https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12
https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag
Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijir Labarai 👇
https://chat.whatsapp.com/KpTjEvHUjd3CVzIQp8CSkZ