Takaitattun Labaran duniya na Yammacin Juma’a 27/10/2023 – 12/04/1445AH

best seller i

Daga Baba Usman Gama

Hukumar EFCC ta kama tsohon gwamnan babban bankin Najeriya Emefiele.

Majalisa ta bukaci a yi gwanjon barikokin ‘yan sanda.

Gwamnan Kano, Abba Kabir Yusuf ya gabatar da kasafin kudin shekrar 2024 daya kai Naira biliyan 350 na sheka 2024 a gaban Majalisar Dokokin Jihar a ranar Juma’a.

Da alama kalaman Rarara cewa Buhari ya lalata Najeriya kafin ya mika wa Tinubu da kuma cewa wata ukun Tinubu sun fi shekaru 8 din Buhari sun fusata masoyansa.

Ƙungiyar masu kiwon kaji a jihar Kano ta sanar da ƙarin farashin kwai sakamakon tashin gwauron zabin da abincin kajin ya yi.

Mutum 4 sun mutu biyo bayan wani hari da yan bindiga suka kai garin Maru, hedkwatar ƙaramar hukumar Maru a jihar Zamfara.

Yan bindiga a jihar Abia sun guntule kan wani jami’in dan sanda a wurin binciken ababan hawa.

ÆŠan daba da rundunar ‘yan sanda ke nema ruwa a jallo a jihar Kano ya miÆ™a wuya tare da wasu ‘yan baranda 40.

Ƙungiyoyi a Nijar za su maka Tinubu a kotu.

Sojojin Amurka sun kai hare-hare ta sama a Syria

Afirka ta Kudu ta fara binciken musabbabin tashin wata mummunar gobara.

Tsohon firaministan China Li Keqiang ya rasu ya na da shekaru 68.

Ivanka Trump za ta bayar da shaida a shari’ar almundahanar kasuwanci a kan mahaifinta da ‘yan’uwanta, kamar yadda wani alkalin New York ya yanke hukunci.

Rikicin Sudan: RSF ta ƙwace iko da birnin Nyala a yankin Darfur.

Ƙungiyoyin ƴan tawayen ƙabilu 3 sun kai hare hare arewacin Myanmar.

An zaɓi Sultan Ibrahim a matsayin sabon sarkin Malesiya.

Golan Bayern Munich Neuer na shirin dawowa bayan jinyar wata 10.

An soke kwantiragin El Ghazi saboda sakon goyon bayan Falasdinu.

Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a

https://twitter.com/Musabestseller?s=09

https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165

https://www.threads.net/@alfijirlabarai

https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12

https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag

Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijir Labarai 👇

https://chat.whatsapp.com/KpTjEvHUjd3CVzIQp8CSkZ

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *