Hukumar Hisbah ta Bayyana Dalili Gayyatar Jaruman TikTok A Kano

TikTok

Darakta Janar na Hisba ta jihar Kano, Sheikh Mujahid Aminuddeen ya ce hukumar tana gayyatar duk wata mace ƴar Tiktok da Facebook zuwa hukumar Hisbah da ke kan titin Sharaɗa Kano.

Alfijir Labarai ta rawaito Hisba ta gayyaci ƴan Tiktok din ne domin yin zama na musamman da Sheikh Daurawa a ranar litinin mai zuwa 6-11-2023 da misalin ƙarfe huɗu na yamma”.

Gayyatar dai na zuwa ne bayan masu amfani da kafafen sadarwa na ta kiraye-kiraye ga hukumar ta tsawatarwa yan Tiktok musamman taurarin Tiktok irinsu Murja Ibrahim Kunya, Mai Wushirya, Al-Ameen G-Fresh da sauransu waɗanda ake ganin ya kamata hukumar ta kwabesu akan yadda suke gudanar da ayyukansu akan shafin Tiktok da Facebook.

Babban Kwamandan ne ake sa ran zai zauna da su ya tattauna da su, yaji menene matsalolin su, duk wacce aure ne matsalarta to zamu Saka ta auren gata na gwamnatin Kano , mai son karatu kuma zamu mayar da ita karatu haka suma Masu son yin sana’o’i zamu tallafa musu don su rika dogaro da kawunansu”. Dr. Mujahid Aminuddeen

Darakta janar din ya kuma ce suna ta samun yabo daga al’ummar jihar kano saboda yadda suka himmatu wajen yakar aiyukan badala a jihar kano baki daya.

” Tun da muka fara wannan aiki na Operation hana Badala muke ta samun yabo, domin babban Kwamandan wannan hukuma ta hisba Yana ta amsa kiraye-kirayen waya daga ciki da wajen kasar nan ana yabawa da aikin da jami’anmu suke gudanar wa.

Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a

https://twitter.com/Musabestseller?s=09

https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165

https://www.threads.net/@alfijirlabarai

https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12

https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag

Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijr Labarai 👇👇

https://chat.whatsapp.com/H47OrRBUPHYEeNqV0vwlQp

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *