Takaitattun Labaran duniya na Yammacin Asabar 04/11/2023 – 20/04/1445AH

best seller i

Daga Baba Usman Gama

Sojojin Najeriya sun yi nasarar bankado wata katafariyar masana’antar kera makamai a jihar Plateau a yau Asabar.

Hedkwatar tsaron Najeriya ta bayyana cewa ragowar kwanakin da suka rage wa ƴan ta’adda a duniya ba su da yawa kuma a kididdige suke.

Tsohon babban hafsan sojin ƙasa Laftanar Janar Tukur Buratai, ya ce rashin tsaro da kasar nan ke fama da shi, ƴan siyasa ne suka samar da shi.

‘Yan sandan jihar Sokoto sunce yan bindga sun kai hari garin Duhuwa, dake karamar hukumar Wurno ta jihar, inda suka kashe mutum 5 tare da jikkata wasu 4.

BUA da Dangote na zargin yi wa juna zagon kasa a harkokin kasuwanci.

Kotun ɗaukaka ƙara da ke zamanta a Legas ta yi watsi da ƙarar da tsohon gwamnan Cross Rivers, Ben Ayade ya shigar na ƙalubalantar nasarar Jarigbe Jarigbe a zaben sanatan Cross Rivers ta Arewa a 2023.

‘Yan bindiga sun sace matan shugaban ƙaramar hukuma a Jigawa.

Masarautar Adamawa ta tuge rawanin hakimin Ribaɗu da ke ƙaramar hukumar Fufore, Alhaji Gidado Abubakar Aliyu.

Kotun ɗaukaka kara ta maida wa Amobi Ogah na LP kujerarsa ta mamban majalisar wakilan tarayya daga jihar Abiya, ta kuma rushe zaɓen ɗan majalisar Udenu/Igboeze, Denis Agbo na LP, inda ta umarci INEC ta canza zaɓe a mazabar cikin kwanaki 90.

Turkiyya ta janye jakadanta daga Isra’ila.

Jam’iyya mai mulki ta NPP a Ghana na gudanar da zaben fidda gwani na shugaban kasa.

An fitar da sunayen jami’an sabuwar hukumar yaki da rashawa ta Nijar.

EPL: Manchester United ta sami nasara akan Fulham da ci 1:0 a wasan yau.

EPL: Manchester city ta sami nasara akan Bounemouth da ci 6:1 a wasan yau.

EPL: Brentford ta sami nasara akan Wolves da ci 3:2 a wasan yau.

Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a

https://twitter.com/Musabestseller?s=09

https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165

https://www.threads.net/@alfijirlabarai

https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12

https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag

Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijr Labarai 👇👇

https://chat.whatsapp.com/H47OrRBUPHYEeNqV0vwlQp

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *