Sauke Abba Kabir daga mulki barazana ce gare mu, Yarabawa mazauna Kano sun koka

yarabawa

Ƙungiyar Yarabawa mazauna jihar Kano sun baiyana fargabar cewar idan har Kotun Koli ta kori Gwamnan Kano, Abba Kabir Yusuf to fa za a iya kai musu hari.

Alfijir Labarai ta rawaito Sakataren ƙungiyar, Taofeek Olalekan Olaosebikon, a taron manema labarai a jiya Alhamis a Kano, ya yi kira ga shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu da kada ya yi katsalandan a kan batun shari’ar zaɓen Kano.

A cewar Olaosebikon, an fara raɗe-raɗin cewa da hannun Tinubu a kokarin da ake na kwace kujerar Gwamna Abba, inda ya ce hakan ka iya zama barazana ga rayuka da dukiyoyin Yarabawa mazauna Kano.

Ya yi kira ga tsohon shugaban kasa, Olusegun Obasanjo da sauran sarakunan Yarabawa a fadin ƙasar nan da su tsawatar wa Tinubu kan yunƙurin tumbuke gwamnatin NNPP a Kano.

“Kowa ya ga cewa Abba ne ya ci zaɓe. To duk wani yunkuri na yin muna-muna ba zai haifar da ɗa mai ido ba kuma mu Yarabawa abin zai shafa tunda shugaban kasar namu ne beyerabe.

Domin Kallon Shirin FATAKE Mai Dogon Zango Season 1 Da Kuma CIgaba Da Kallon Season 2, Danna wannan Link din👇

https://youtube.com/@ukentertainmentkano?si=PPtuxJz76OuNP_oI

“Saboda haka muna kira ga Tinubu da ya bari kotu ta yi aikin ta kuma ya bari a samu zaman lafiya a Kano, domin idan rikici ya barke, to fa mu za a hara,” in ji Olaosebikon.

Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a

https://twitter.com/Musabestseller?s=09

https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165

https://www.threads.net/@alfijirlabarai

https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12

https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag

Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijr Labarai 👇👇

https://chat.whatsapp.com/H47OrRBUPHYEeNqV0vwlQp

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *