Hukumar Kula da filayen Jiragen sama ta Ƙasa (FAAN) ta haramta amfani da jakar tafiye-tafiye da aka fi sani da Ghana Must Go ga matafiya masu amfani da filayen jiragen saman kasar.
Alfijir labarai ta rawaito cewa, dokar ta shafi masu tafiya ta filayen jiragen sama na kasa da kasa.
FAAN ta ce amfani da jakar Ghana Must Go a matsayin harkar tafiye-tafiye na jawo manyan kamfanonin jiragen sama asara tare da lalata na’urar daukar kaya.
FAAN ta bayyana hakan ne a wata sanarwa mai taken, ‘ Hana Amfani da Ghana Must Go’ mai dauke da sa hannun Manaja, Ma’aikatar Jiragen Sama, Henok Gizachew da kwanan wata 24 ga Nuwamba.
An ba da sanarwar ne ga kamfanonin jiragen sama masu amfani da filayen jiragen sama na kasa da kasa yayin da kamfanonin jiragen suka sanar da abokan hulɗarsu da fasinjoji.
Daya daga cikin kamfanonin jirgin a cikin wani sako ga fasinjojin ya ce, “Ana sanar da mu cewa daga ranar 25 ga Nuwamba, 2023, an haramta amfani da Ghana Must Go’ don tafiya a cikin jirginmu.”
Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a
https://twitter.com/Musabestseller?s=09
https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165
https://www.threads.net/@alfijirlabarai
https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12
https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag
Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijr Labarai 👇👇
https://chat.whatsapp.com/H47OrRBUPHYEeNqV0vwlQp